Akwai alamun cewa tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, na iya bai wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour party a zaben 2023, Peter Obi, damar tsayawa tare da shi a matsayin mataimaki a takarar shugaban kasa karkashin tikitin hadin gwiwa da nufin yin wa’adi guda kacal.
Wata majiya mai tushe daga cikin wadanda ke cikin shirin hadin gwiwar, wacce ta nemi a sakaya sunanta saboda rashin bata izini Magana kan batun, ta shaida wa jaridar The PUNCH cewa an fara tattaunawa a kan wannan matsaya ne a lokacin wani taro tsakanin Atiku da Peter Obi da aka gudanar tun farkon wannan shekara a kasar Birtaniya.
Majiyoyin sun bayyana cewa Atiku ya amince da yin wa’adi guda na shekara huɗu, kuma Obi ya amince da kasancewa dan takarar mataimakin shugaban kasar.
Sai dai rahotanni na nuni da cewa tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, yana kokarin samun cikakken goyon bayan magoya bayansa na kusa kafin ya amince da tsayawa takarar.
A zaben shugaban kasa na 2019, Obi ya kasance mataimakin Atiku karkashin jam’iyyar PDP, inda tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC yayi nasarar akan su.
A ranar 20 ga Maris, Atiku, da Obi, da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai, da wasu shugabannin siyasa, sun bayyana hadin gwiwar sabuwar jam’iyyar adawa a birnin Abuja, domin kalubalantar shugaban kasa mai ci Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.