Atiku ya musanta amfana da kwangilar dake tsakanin kamfanin dake lura da jiragen ruwa da kuma Gwamnatin tarayya

0 160

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya musanta cewa babu wani abu da ya amfana dangane da dawo da kwangilar dake tsakanin kamfanin  dake  lura da jiragen ruwa da kuma Gwamnatin tarayya.

Atiku Abubakar, a shafin sa na X (wanda aka fi sani da twitter), ya ce ya sayar da hannun jarinsa a kamfanin da ya kafa, inda ya kara da cewa hakan baya nufin kamfanin yaja baya ba.

Martanin tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya biyo bayan wata takarda da hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya ta yi na maido da kamfanin Intels a matsayin hukumar kula da ayyukan jiragen ruwa na hukumar a gundumomin jiragen.

Takardar mai dauke da kwanan watan 30 Nuwamba 2023, ta ce maido da aikin ya biyo bayan umarnin shugaban kasa ne, Ya kuma kara da cewa mayar da aikin ya biyo bayan hukuncin da wata kotu ta yanke a jihar Legas a ranar 21 ga watan Satumba 2023. Da yake mayar da martani game da rade-radin da ya ke samu akan dawo da kamfanin, Atiku ya ce, a watan Janairun 2021, ya bayyana cewa ya sayar da hannun jarin sa

Leave a Reply

%d bloggers like this: