Mazauna wani kauye a jihar Kaduna sun tsere daga gidajen su saboda barazanar tsaro
Mazauna kauyen Maganda dake unguwar Magajin Gari Uku a karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna, sun tsere daga gidajensu sakamakon janye jami’an tsaro da aka girke a yankin.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu mazauna kauyukan sun fice saboda fargabar hare-haren ‘yan bindiga da suka shafe shekaru suna addabar al’ummar yankin.
Mazauna yankin sun ce jami’an tsaron da aka tura domin kare mutanen kauyen sun bar yankin ne a ranar Asabar din da ta gabata ba tare da an sanar da su ba, lamarin da ya haifar da rudani a tsakanin mazauna garin.
Wani mazaunin yankin kuma tsohon kansila mai suna Ismail A. Ahmed, ya bayyana cewa tuni ya kwashe iyalansa daga yankin.
Inda ya ce da zarar jami’an tsaro sun fita daga yankin sai ‘yan fashin su rinka bi gida-gida suna karbar wayoyin mutane da kudadensu. Ya ce galibin mutanen kauyen sun tsere daga gidajensu, inda suka bar amfanin gonakinsu da sauran kadarori.