Kungiyar Lauyoyin Mata ta Duniya (FIDA) ta ce ta gurfanar da wasu mutane 28 da ake zargi da aikata laifukan fyade a jihar Yobe a cikin watanni 11 da suka gabata.
Shugabar kungiyar a jihar Yobe, Barista Hannatu Farouk ce ta bayyana hakan ga manema labarai a lokacin shari’ar da ake yi Damaturu babban birnin jihar Yobe .
Ta ce yayin da aka yankewa wasu da ake zargi da aikata fyaden, fiye da mutane 30 sun yi shawarwari ba tare da kotu ba, wanda aka sasanta rikicin. A cewarta, dokar kare yara za ta rage aurar da yara kanana da cin zarafin mata a jihar ta Yobe.