Ba za a samu zaman lafiya a Arewa nan da Shekaru 10 ba” Uba Sani ya jero Dalilai 3”

0 495

Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya ce talauci, matsin tattalin arziki da rashin aikin ne tushen matsalar tsaron da ake fama da ita a Arewa Malam Uba Sani ya ce matukar shugabannin Arewa ba su haɗa hannu wuri ɗaya ba, yankin zai ci gaba da fuskantsar matsaloli Gwamnan ya ce lokaci ya yi da za a daina amfani da ƙarfin soji kaɗai domin sai an magance rashin aikin yi da talauci kafin a yi nasara.

Kaduna – Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana cewa talauci da matsin tattalin arziki na daga cikin manyan dalilan da ke kawo matsalar tsaro a Arewacin Najeriya. Ya ce sai an fuskanci wadannan matsaloli ta hanyar hadin gwiwa da tsari mai kyau, in ba haka ba, yankin zai ci gaba da fuskantar rikice-rikice.

Leave a Reply