Tsohon shugaban kasar Amurka Joe Biden ya kamu da cutar Kansar mafitsara kamar yadda ofishinsa ya fitar da sanarwa.
Tsohon shugaban da iyalansa na nazari kan matakin maganin cutar tare da kwararrun likitoci.
A sanarwar da ofishin Mr Biden ya fitar ya ce ya je asibiti domin yi masa gwaje-gwaje sakamakon matsalar da ya ke samu wajen yin fitsari, anan ne likitoci suka gano Kansar mafitsara ce ke damunsa.
Bayan karin gwaji, aka tabbatar ya kamu da mummunar nau’in cutar kansar mafitsara da ta fara yaɗuwa zuwa kashinsa.
Likitocin sun ce duk da munin nau’in kansar amma sauyin da ake samu na jikin mai dauke da ita ba zai hana yin maganinta da saurin karbar sauyin ga jikin dan adam ba.
Rahotanni sun ce iyalan Mr Biden na duba nau’in maganin da za a yi ma sa tare da shawarar likitocinsa.
Tuni jiga-jigan jam’iyyar Democrat a sassan Amurka suka fara wallafa sakonnin karfafa gwiwa.
Shugaba Trump ya ce bai ji dadin labarin halin da Biden ke ciki ba, ya na kuma yi masa fatan samun sauki cikin gaggawa. Shima tsohon shugaban Amurka kuma na hannun daman Mr Biden Barrack Obama ya wallafa a shafinsa na X cewa shi da maidakinsa Mixchelle na tare da iyalan Biden a irin wannan lokaci.