

- Gwamna Zulum ya raba wa likitoci fiye da 80 didaje da kudi Naira miliyan 79 don inganta rayuwarsu - July 2, 2022
- Manyan Sarakunan kasar Yarabawa sunyi kiran samun zaman lafiya daga gwamnati kafin zaben 2023 - July 2, 2022
- Kasar Jamus za ta fara dawo wa da Najeriya dubban kayayyakin tarihin ta da aka wawushe tun lokacin mulkin mallaka - July 2, 2022
Jam’iyyar APC mai mulki za ta fara tantance dukkan ‘yan takararta na shugaban kasa na tsawon kwanaki biyu daga yanzu.
Za a gudanar da aikin ne a otal din Hilton Transcorp dake Abuja gabanin zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar a ranar 6 ga watan Yuni.
Wata majiya mai tushe daga jam’iyyar ta ce tsohon shugaban jam’iyyar na kasa Cif John Odigie Oyegun ne zai jagoranci kwamitin tantance mutane bakwai na shugaban kasa.
Wadanda za a tantance sun hada da, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, mataimakin shugaban kasa Yemi Osibanjo, tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi, tsohon ministan raya yankin Neja Delta, Godswill Akpabio, tsohon ministan kimiyya da fasaha da Dr Ogbonnaya Onu, tsohon gwamnan Imo Sanata Rochas Okorocha da tsohon Gwamnan Ogun, Sen. Ibikunle Amosu.
Sauran sun hada da tsohon shugaban majalisar dattawa, Sen. Ken Nnamani, gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, gwamnan Jigawa Mohammed Badaru Abubakar, tsohon gwamnan Zamfara Sen. Ahmed Yerima da shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan.