

- Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta rufe kamfanonin ruwa guda 10 a jihar Ondo bisa rashin bin ka’idoji - July 4, 2022
- Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AA, Hamza Al-Mustapha, ya ce jam’iyyarsa ba za ta yi hadin gwiwa da mutanen da basu damu da makomar al’umma ba - July 4, 2022
- Yadda wani mutum ya kona matarsa bayan ya gama dukanta a jihar Ogun - July 4, 2022
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, ta sake bankado wasu makudan kudade har Naira biliyan 90 da ake zargin dakataccen Akanta Janar na Tarayyar, Ahmed Idris da hannu a ciki.
Idris wanda ke neman beli a daren jiya, rahotanni sun ce ya yi magana kan wasu manyan jami’an gwamnati da ke da hannu a wasu hada-hadar kasuwanci da badalakar kudade.
A ci gaba da fadada binciken da hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC takeyi.
Ahmed Idriss ya bayyana cewa,wadanda ke da hannu a nadakalar sunhada da hannun tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdul-Azeez Yari.
Da wannan karin kudin da ake zargin Ahmed Idriss da badakalarsu yanzu kudaden sun kai naira biliyan 170.
Hukumar ta EFCC ta kuma gurfanar da wani babban sakatare a gaban kuliya dangane da wasu yarjejeniyoyin da ke da hannu a ciki.