Kungiyar kiristoci ta kasa CAN ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya taimaka wajen kubutar da shugaban cocin Methodist Church ta kasa, mai martaba Samuel Uche da wasu mutane biyu daga hannun masu garkuwa da mutane.

An rahoto cewa an sace Uche ne a jiya a karamar hukumar Umunneochi ta jihar Abia tare da Reverend Dennis Mark, Bishop Methodist na Owerri, wanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka sace su.

Idan zamu iya tunawa dai Yan bindiga sun yi garkuwa da malaman jami’oi akalla 10 a shekarar 2022 kadai.

Kuma babu ko daya daga cikinsu wanda jami’an tsaro suka ceto.

Kazalika akwai malama jami’oin da yan bindaga suka kashe su, bayan sunyi garkuwa da su.

A cikin wata sanarwa da CAN ta fitar a yau kuma mai dauke da sa hannun mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai da sadarwa ga shugaban CAN, Fasto Adebayo Oladeji, kungiyar ta Kirista ta bukaci Buhari da ya umurci jami’an tsaro da su kubutar da shugaban darikar Methodist da abokansa cikin gaggawa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: