Hukumar Kula da Hasashen Yanayi ta bukaci yan Najeriya da su kasance cikin shiri domin fuskantar matsanancin zafi na tsawon kwanaki uku

0 80

Hukumar Kula da Hasashen Yanayi ta kasa NiMet ta bukaci yan kasar nan da su kasance cikin shiri domin fuskantar matsanancin zafi na tsawon kwanaki uku masu zuwa a wasu sassan kasarnan.

Babban daraktan hukumar Farfesa Mansur Matazu ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da suka fitar mai dauke da sa hannunsa.

Ya ce ana sa ran za a iya samun zafi tsakanin ma’unin Salshiyos 35 zuwa 40 a yawancin sassan garuruwan Arewa.

Sai dai ta ce sassan jihohin Kebbi, Sokoto, Zamfara, Katsina, Kano, Jigawa, Bauchi, Gombe, Yobe, da Borno ana sa ran za su fuskanci zafi sama da ma’aunin Salshiyos 40.

Hasashen ya kuma bayyana cewa anfara samun zafi a wasu bangarorin Kebbi, Sokoto, Katsina, Kano, Dutse, Nguru, da Maiduguri tin daga jiya Lahadi.

A gobe kuwa 31 ga Mayu na 2022, ana sa ran sassan Kebbi, Sokoto, Zamfara, Katsina, Kano, Jigawa, Bauchi, Gombe, Yobe, da Borno za su fuskanci matsanancin zafi na sama da Salshiyos  40.

Leave a Reply

%d bloggers like this: