Babban safeton yan sanda na kasa ya gargaɗi wasu gwamoni da ake zargi na daukar nauyin ‘yandaba domin ingiza rikici

0 106

Babban safeton yan sanda na kasa ya gargaɗi wasu gwamoni da ake zargi na daukar nauyin ‘yandaba domin ingiza rikici.

Safeton yan sandan ya bayyana haka jiya yayin zaman ganawa a helkwatar tsaro ta kasa da ke Abuja, inda ya bukaci shugabannin jam’iyyu da zasu ja kunnen magoya bayan su wajen tada zaune tsaye, ya na mai cewa dukkan wanda aka kama da hakan zai fuskanci hukunci

Usman Baba, ya ce suna samun rahotanni sosai daga jihohi kan yadda wasu gwamnoni ke karfafa dabanci tsakanin matasa da kai wa ‘yan hamayya hari.

Usman Baba, ya ce za su dau mataki mai tsauri domin daƙile duk wani yunkuri yada kiyayya ko haddasa rikici bisa tanadin dokokin kasar.

Jami’in ya kuma umarci ‘yan takara musamman masu neman kujerar shugaban kasa su mutunta yarjejeniyar da suka sanyawa hannu na tabbatar da zaman lafiya kafin zabe da lokacin zabe da kuma bayan zabe.

Shugaban hukumar leken asiri, Maj.-Gen. Samuel Adebayo  da Darakta-Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Ahmed Rufa’i, na daga cikin wadanda suka halarci zaman, sun gargadi  daukacin shugabannin jam’iyyar siyasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: