Shugaba Buhari ya amince da karin albashi da walwala ga jami’an shari’a na Najeriya

0 76

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da karin albashi da walwala ga jami’an shari’ar kasar nan.

Shugaba Buhari ya bayyana haka jiya a Fatakwalal babban jihar Ribas yayin bikin bude makarantar horas da lauyoyi a Fatakwal da aka gina karkashin gwamnatin gwamna  Nyesom Wike na jihar Ribas.

Shugaba Buhari da ya samu wakilcin Ministan Shari’a Abubakar Malami SAN, yace inganta tsarin jindadin ma’aikatan shari’a da sauran tsare-tsare an yi sune domin karfafa ikon ma’aikatar domin itace ganshikin dimokaradiyya

Shugaban, ya kuma umarci shugaban hukumar tattara haraji ta kasa da babban alkalin alkalai na kasa da a dauki matakan gaggawa wajen ganin an fara aiwatar da wanna umarnin

Leave a Reply

%d bloggers like this: