Masu karamin karfi 3,266 ne za su ci gajiyar shirin J-cares na musayar kudi 10,000 a jihar Jigawa

0 87

Masu karamin karfi dubu 3,266 ne za su ci gajiyar shirin J-cares na musayar kudi na naira dubu goma a jihar Jigawa.

Mutum goma sha daya ne za su amfana daga kowane gundumomin zabe dari biyu da tamanin na fadin jihar Jigawa.

Sakataren zartarwa na hukumar farfadowa da jihar Dr. Ibrahim Rabakaya ya bayyana hakan a cikin shirin gidan rediyon Jigawa kai tsaye.

Ya ce shirin wanda zai dauki tsawon shekaru biyu ana gudanar da shi, zawarawa, talakawan Birane, nakasassu, tsofaffi da masu fama da rashin lafiya a matsayin wadanda suka ci gajiyar shirin.

Dokta Rabakaya ya ce shirin da zai fara nan ba da dadewa ba, za a sanya ido sosai don tabbatar da cewa wadanda aka zaba kawai za su ci gajiyar shirin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: