Rundunar ‘yan sandan jihar Neja tayi nasarar kashe ‘yan bindiga bakwai a kauyen Kumbashi da ke karamar hukumar Mariga

0 96

Rundunar ‘yan sandan jihar Neja tayi nasarar kashe ‘yan bindiga bakwai a kauyen Kumbashi da ke karamar hukumar Mariga a jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ogundele Ayodeji ne ya tabbatar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labara na kasa NAN a babban biornin jihar Minna jiya Alhamis.

Ayodeji ya yi nadamar yadda wasu ‘yan kungiyar ’yan banga biyu suka samu raunukan harsashi kuma an kai su babban asibitin Kontagora domin yi musu magani.

Hakazalika, rundunar ‘yan sandan ta kama wasu mutane 17 da ake zargin ‘yan bata-gari ne a sassa daban-daban na kananan hukumomin Chanchaga da Bosso na jihar.

Kafin hakan dai ya ce, a ranar 5 ga watan da muke ciki, wasu bata gari da ke kewayen Angwan-Daji da Limawa, sun yi artabu da muggan makamai, kuma a sakamakon haka aka kashe wani Ashiru Tofa na yankin Limawa har lahira.

Ayodeji ya ce, rundunar ‘yan sandan ta samu nasarar cafke wasu mutane 17 da ake zargin ‘yan ta’adda ne a yankin Angwan-Daji da kuma Limawa.

Ya ce za a gurfanar da duk wadanda ake zargin a gaban kuliya domin a tuhume su bayan bincike.

Leave a Reply

%d bloggers like this: