Za mu magance dukkan matsalolin da suka shafi rajistar masu zabe ta kasa – INEC

0 87

A wani bangaren kuma, gabanin babban zaben na shekarar 2023, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa a jiya Alhamis ta ce za ta magance dukkan batutuwan da suka shafi rajistar masu zabe ta kasa.

Hukumar ta INEC dai a wannan wata ne ta bayyana daukacin rajistar jama’a a shafinta na yanar gizo a karon farko a tarihin zaben kasar.

Sai dai da yawa daga cikin ‘yan Najeriya sun gano adadin masu jefa kuri’a da ba su kai shekaru ba, da kuma masu rajista fiye daya.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan hukumar na kasa Festus Okoye, INEC ta ce ta dukufa wajen tsaftace rijistar tare da hukunta duk wanda aka samu da laifin zamba cikin aminci.

Hukumar ta ce bayyana rajistar a bainar jama’a manuniya ce ta cewar ta shirya gaskiya da adalci a bangarenta.

Ana sa ran za a fitar katunan zaben a zahiri a matakin Rajistar daga ranar 12 zuwa yau 18 ga Nuwamba.

A matakin kananan hukumomi, za a baje kolin daga ranar 19 zuwa 25 ga Nuwamba, inda masu kada kuri’a za su iya yin korafi da yan gyare-gyare na wasu daga cikin bayanan da aka riga aka tura.

Leave a Reply

%d bloggers like this: