Labarai

Babban sufeton ‘yan sandan Najeriya ya bada kudi sama da naira miliyan 30 da dubu 200 ga iyalan ‘yan sanda takwas da suka mutu a bakin aiki

Babban sufeton ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali ya gabatar da Cek din kudi na sama da naira miliyan 30 da dubu 200 ga iyalan ‘yan sanda takwas da suka mutu a bakin aiki.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara Ayuba Elkanah ne ya gabatar da Cek din a madadin babban sufeton ‘yan sandan jihar, jiya a Gusau babban birnin jihar Zamfara.

Ayuba Elkanah yayi nuni da cewa kudin ya kasance shaidar shirin Sufeto-Janar na ‘yan sanda na tabbatar da walwala da jin dadin iyalan jami’an ‘yan sandan da suka mutu a bakin aiki.

Ya kuma yabawa Sufeto-Janar na ‘yan sandan bisa wannan karimcin tare da bayyana hakan a matsayin wanda ya dace, yana mai cewa hakan zai taimaka matuka wajen rage radadin da iyalan jami’an ‘yan sandan da suka rasu suke ciki.

Kwamishinan ‘yan sandan ya tabbatar da jajircewar jami’an ‘yansandan, wadanda ya ce za su ci gaba da gudanar da ayyukansu domin samar da zaman lafiya da tsaro a jihar Zamfara dama Najeriya baki daya.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: