Gwamnan jihar Jigawa Badaru Abubakar na cigaba da taya Bola Ahmed Tinubu murnar lashe zaben fidda gwanin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC

0 83

Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, ya taya Bola Ahmed Tinubu murnar lashe zaben fidda gwanin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.

Sakon taya murnan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga gwamnan kan sabbin kafafen yada labarai, Auwalu Danladi Sankara ya fitar a jiya.

Gwamna Badaru wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na farko a cikin gwamnonin da suka janyewa tsohon gwamnan jihar Legas, ya kuma yabawa sauran masu neman tsayawa takarar shugabancin kasarnan bisa jajircewarsu.

Gwamna Badaru ya bi sahun wasu ‘yan takarar shugaban kasa kamar gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi da tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom Godswill Akpabio da tsohon gwamnan jihar Ogun Ibikunle Amosun inda suka janyewa Bola Ahmad Tinubu.

Gwamna Badaru ya yi alkawarin sadaukar da lokacinsa da dukiyarsa wajen hada kai da yi wa Bola Ahmed Tinubu yakin neman zabi da tabbatar da nasarar jam’iyyar APC a jihar Jigawa da Najeriya baki daya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: