Kimanin ‘yan Najeriya dubu 1 da 834 ne suka mutu sakamakon hadurran ababen hawa a cikin watanni ukun farko na shekarar 2022.

Hakan na zuwa ne a wani rahoto da hukumar kididdiga ta kasa ta fitar jiya a Abuja.

Rahoton ya ce mutane dubu 24 da 192 ne suka gamu da hadura dubu 5 da 316 cikin watannin, inda mutane dubu 12 da 124 suka samu raunuka.

Rahoton ya dora alhalin haduran dubu 2 da 561 akan gudun wuce kima, sai hadura 290 akan wuce ababen hawa ba bisa ka’ida ba, da hadura 243 akan rashin kiyayewa da alamun tukin ababen hawa na gefen hanya.

Dangane da jinsin mutanen da suka mutu a haduran ababen hawan, maza dubu 1 da 487 ne suka mutu a cikin watannin, wanda ya kai kashi 81 cikin 100 na mutane dubu 1 da 834 da suka mutu gaba daya.

A daya hannun kuma, matan da suka mutu sun kai 347, wanda ya kai kashi 19 cikin 100 na mutane dubu 1 da 834 da suka mutu a jumlace.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: