Shugaban hukumar NDLEA Buba Marwa ya bukaci yin gwajin kwaya kan matasa masu yin NYSC kafin su fara aikin

0 59

Shugaban hukumar yaki da sha da fataucin muggan kwayoyi ta kasa NDLEA, Buba Marwa ya bukaci yin gwajin kwaya kan matasa masu yiwa kasa hidima kafin su fara yi wa kasa hidima na shekara daya idan suka je sansanonin basu horo daban-daban.

Buba Marwa ya yi wannan kiran ne jiya a yayin ziyarar ban girma da Darakta Janar na hukumar matasa masu yiwa kasa hidima, NYSC, Birgediya Janar Mohammed Fadah ya kai masa a Abuja.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na Hukumar NDLEA, Femi Babafemi ya sanyawa hannu kuma ya fitar a jiya.

Buba Marwa ya ce gwajin kwayar ya zama dole kan matasa masu yiwa kasa hidima kafin su fara yi wa kasa hidima na shekara daya idan suka je sansanonin basu horo daban-daban.

Hakan, in ji shi, wani bangare ne na kokarin rage shaye-shayen muggan kwayoyi da hukumar ke yi.

Buba Marwa ya bayyana matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi a Najeriya ta hanyar amfani da bayanan binciken da aka gudanar a shekarar 2018 kan shaye-shaye, inda ya yi kira da a yi kokarin ganin an kawo sauyi akan matsalar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: