Babu ruwa na da harkallar kudin makamai inji Buratai

0 188

Tsohon babban hafsan sojojin Najeriya, Tukur Buratai ya bayyana cewa babu ruwan sa da harkallar Dala Biliyan daya da aka fidda don siyan makamai.

A wata takarda da wanda lauyan sa, Osuagwu Ugochukwu, ya ska wa hannu, Buratai ya ce a iya sanin sa bai sanda wani dala biliyan 1 da aka taba bashi wai na makamai kuma tsoffin manyan hafsoshin Najeriya suka yi awon gaba da su ba.

” Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Mungono wanda aka danganta wannan kalamai da shi ya ce ba haka ya fadi ba. Saboda haka muna kira ga mutane su daina cewa wai su Buratai sun waske da kudin makamai.

A karshe lauyan ya gargadi masu ci gaba da yayada wannan magana da babu gaskiya a cikin ta cewe kotu ce za ta raba su.

Yadda aka aka yi wa kudin makamai cin-kaca a karkashin su Buratai –Monguno, Mashawarcin Buhari

“Wannan gaskiya ce tabbas cewa an ware bilyoyin nairori domin sayen kayan makamai a zamanin wannan gwamnatin, amma wadanda aka damka wa alhakin kudaden sun ragargaje su, an nema ko sama ko kasa, an rasa inda kudin su ke.”

Mashawarcin Buhari a Harkokin Tsaro, Babagana Monguno, ya fallasa cewa an ware wasu kudade a karkashin wannan gwamnatin domin sayen makamai a karkashin Manyan Hafsoshin Tsaron da su ka sauka kwanan nan, amma an ragargaje kudin, ko albarushi ba a sawo da kudaden ba.

Haka da Mashawarcin kan Harkokin Tsaro, kuma Manjo Janar Mai Ritaya Babagana Monguno ya bayyana, a wata tattaunawa da ya yi da BBC a ranar Juma’a.

Babagana ya fallasa wannan satar kudade wata daya bayan Buhari ya sauke manyan hafsoshin tsaron, cikin su har da Tukur Buratai.

Makonni biyu bayan sauke su, sau kuma Buhari ya sake yi masu wata sakayyar da aikin jakadanci zuwa wasu kasashen da har zuwa yau dai ba a bayyana kasashen da aka tura kowanen su ba.

A wannan fallasa mai ban-mamaki, Monguno ya ce yayin da wadannan sabbin manyan hafsoshi su ka kama aiki, sun nemi makaman da su ka kamata a sawo da makudan kudaden, amma ko albarushi babu.

Haka nan kuma sun nemi inda aka ajiye makudan kudaden, nan ma ko karfanfana ba su samu ba.

Yayin da ya kara da cewa ba sata ya kala wa su Buratai ba, to amma dai an nemi kudaden babu, kuma babu makaman da ya kamata a ce sun sawo da kudaden.

“Yanzu dai sabbin Manyan Hafsoshin Tsaro sun kama aiki. Amma kuma sun rasa inda kudaden da aka ware wa tsoffin hafsoshin da aka cire su ke, domin dai ba a sawo makaman da kudaden ba.” Inji Monguno

“Ina tabbatar maku cewa Shugaban Kasa lallai zai binciki inda kudaden su ke. Su ma Gwamnonin Najeriya su na mamakin yadda aka yi da kudaden. Amma ina tabbatar maku Shugaban Kasa zai sa a yi bincike.”

“Yanzu dai binciken farko ya tabbatar da cewa babu kudin, kuma babu makaman da aka ware kudin domin su.”

Leave a Reply

%d bloggers like this: