A ranar Asabar ne illahirin shugabannin darikar Tijjaniya suka amince da nadin tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a matsayin sabon jagoran darikar Tijjaniya a kasar nan.
Kakan sarki Sanusi ne jagoran darikar Tijjaniya na farko a Najeriya. Bayan shi sai marigayi Isiyaka Rabiu wanda tun bayan rasuwar sa ba nada sabon khalifa ba.
Idan ba a manta ba an samu rarrabuwar kai a tsakanin mabiya daikar Tijjaniya a zamanin jagorancin marigayi Isiya Rabiu.
Darikar ta rabu kashi biyu, bangaren Isyaka Rabiu da kuma bangaren Babban malami Sheikh Dahiru Bauchi.
Kowane bangare na yin gaban kansa ne ba tare da yadda dayan su shine jagora ba.
Wannan nadi na sarki Sanusi ya kawo hadin kai a tsakanin mabiya darikar wanda ita ce darika mai yawan mabiya a kasar nan da Nahiyar Afirka.
Manyan malaman darikar Tijjaniya, daga kasashen Afirka da dama sun halarci wannan taron nadi a Sokoto.
Hakazalika wannan nadi da aka yi wa Sarki Sanusi zai kara masa dara, kuma yawan mabiya, sannan kuma da lula shi can kololuwa wajen karfi da daraja ko a siyasan ce.
Biyayya ga jogoran darika na da matukar muhimmanci wand a dalilin haka dole idan a Arewa zaka nemi wani abu, alakarka da jagoran Darikar Tijjaniya zai yi matukar yi maka tasiri.
A wurin taron, shida kansa Khalifan Ibrahim Inyass ne ya jagoraci naɗa tsohon sarkin.
Shi da kansa Dabiru Bauchi da manyan malaman darikar sun halarci taron kuma sun yi ma’am da nadin Sanusi a matsayin Jagoran darika Tijjaniya na Najeriya.