Baffa Bichi ya fito fili ya soki gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf

0 123

Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Dr. Abdullahi Baffa Bichi, ya fito fili ya soki gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, yana zarginta da rashin gaskiya da kuma cin hanci da ya zarce na gwamnatin da ta gabata.

A cikin wani faifan bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, Dr. Baffa Bichi ya ce gwamnatin yanzu ta tafka kura-kurai da laifuka da suka fi na tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje, wanda shima aka yi ta zargi da cin hanci a lokacin mulkinsa na shekaru takwas.

Ya kara da cewa halin da ake ciki a yanzu ka iya hana gwamnatin Yusuf kai wa zaben shekara ta 2027, yana mai cewa shi da kansa zai jagoranci tona asirin abin da ya kira miyagun ayyuka da ake aikatawa a cikin gwamnatin.

A ‘yan makonnin da suka gabata, Dr. Bichi da wasu mutum 14 sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC, inda aka tarbe su hannu bibbiyu daga shugabannin jam’iyyar a matakin jiha da na kasa.

Gwamnatin Kano ta yanzu ta bayyana cewa ta sallami Dr. Bichi ne saboda dalilan lafiya, sai dai jama’a da dama na nuna shakku da tantama kan hakan, musamman ganin yadda ake zargin ya ja Gwamna Abba Kabir gaba da jagoran siyasar sa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Leave a Reply