Rikicin Addini yayi sanadiyar mutuwar mutane 100 a Siriya

0 510

Mutane sama da 100 sun mutu a cikin kwanaki biyu da aka kwashe ana gwabza rikicin addini a Syria, kamar yadda kungiyar kare hakkin ɗan adam ta Syrian Observatory, wadda ke sa ido akan yaƙin da ake yi a ƙasar ta bayyana.

Ƙungiyar da ke zaune a Birtaniya, wadda ta dogara akan majiyoyi daga Syria wajen samun bayanai, ta ce adadin mutane da suka mutu a rikicin yankunan Jaramana da Sahnaya na Damascus, babban birnin ƙasar, sun hada da jami’an tsaro 30 da mayaƙan Musulmi masu bin aƙidar Druze 15, da   farar hula guda.

A kudancin lardin Suweda, an kashe mayaƙan Druze 27, kuma 23 daga cikin su ta hanyar kwanton ɓauna aka halaka su akan hanyar Suweda zuwa Damascus a wannan Laraba, kuma ana ganin za  a samu ƙarin waɗanda lamarin ya rutsa da su.

Masu aikin ceto sun ce, rikicin kwanaki biyun ya ɓarke ne sakamakon wata murya da aka naɗa, wadda ke yin ɓantanci ga annabi Muhammad S.W.A, wadda ta karaɗe shafukan sada zumunta, muryar da jagororin ƙungiyar suka ce ƙirƙirar ta aka yi.

A jiya alhamis ne, jagoran mabiya mazahabar Druze a Syria, Sheikh Hikmat al-Hijri, ya yi tir da abin da ya kira gangamin ƙare dangi da ake yi akan al’ummarsa.

Leave a Reply