tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi watsi da fom na takarar shugaban kasa da wata kungiya daga Arewacin kasarnan ta saya masa.

Goodluck Jonathan ya bayyana saya masa form ba tare da sahalewarsa da cewa cin zarafi ne.

Cikin wata sanarwa da kakakinsa, Ikechukwu Eze, tsohon shugaban kasa ya kuma ce har yanzu bai gama yanke shawarar sake neman shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC mai Mulki ba.

An bayar da rahoton yadda wata kungiyar Arewa ta sayi fom saboda Goodluck Jonathan wanda har yanzu bai tabbatar da ko zai tsaya ko ba zai tsaya takarar shugaban kasa ba.

Sai dai, kakakin nasa, Ikechukwu Eze, ya fada cikin sanarwar tasa cewa ba a tuntubi tsohon shugaban kasar ba, kafin a saya masa form din.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: