Barcelona Zata Cefanar Da Ƴan Wasa 12

0 194

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ta shirya sauraron tayin masu bukatar yan wasan ta har kusan 12 da zarar an bude kakar wasanni ta bana.

Tuni har masu sharhin wasanni suka fara alaƙanta cefanar da yan wasan ne saboda kokarin kawo dan wasan gaba na Inter Milan Lautaro Martinez.

Daga cikin yan wasan da za a kadawa kararrawar dai akwai; Dembele da Coutinho, Samuel Umtiti, Junior Firpo, Ivan Rakitic, Neto, Nelson Semedo, Arturo Vidal, Martin Braithwaite, Carles Alena, Rafinha Alcantara da kuma Jean-Clair Todibo.

Shugaban ƙungiyar Jose Bartomeu ya zanta da mahukunta a kungiyar Inter Milan din kan ɗaukar ɗan wasan ɗan asalin ƙasar Argentina.

Barcelona dai na cikin ƙaƙanakayi ta fuskar samun kuɗin shiga sanadiyyar annobar Korona, don haka kuɗin da zasu kashe ba shi da yawa kan yan wasa.

Jaridar Marca ta rawaito cewa Barcelona zata sanya kusan rabin yan wasanta a kasuwa don samun kuɗaɗen shiga da kuma samun zarafin kawo sabbin fuska kungiyar.

Amma sai dai sanarwar ta bayyana cewa ba duk yan wasan 12 ne zasu tafi a matsayin tafiyar din-din ba, wasu daga cikinsu zasu tafi ne a matsayin aro.

Leave a Reply

%d bloggers like this: