Sarkin musulman Najeriya, Alhaji Sa’ad Abubakar ya bayyana ranar juma’a 31 ga watan da muke ciki a matsayin ranar sallar idi babba, tare da bukatar al’ummar musulmi su gudanar da sallar Idin a masallatan juma’a ba’a wajajan da aka saba gudanar da sallar idi ba.

Alhaji Sa’ad Abubakar yayi wannan kiran ne cikin sanarwar da shugaban kwamitin al’amuran addini, Sambo Junaidu ya fitar, a yayin ganawa da sarkin musulman yayi da yan Jaridu a jiya Alhamis a Sakkwato.

Sarkin musulmin yayi fatan kiyayewar ubangiji da albarkar sa ga al’ummar Najeriya baki daya.

Ya kuma bukaci al’ummar musulmai da su cigaba da addu’ar zaman lafiya, da kuma cigaba ga kasar Najeriya a yayin sakon sa na taya murnar sallah.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: