Bayan Warkewa Daga Korona Za’a Mayar Da Almajirai 64 Jihohinsu

0 95

Gwamnatin jihar Niger ta bayar da sanarwar cewa Almajirai 64 da akayiwa gwaji ya nuna suna dauke da cutar COVID-19 a jihar, sun samu lafiya za’a kuma maida su zuwa ga iyayan su.

Kwamishinan lafiya da ayyukan asibitoci na jihar Dr Muhammad Makusidi shine ya bayyana haka a lokacin da yake amsa tambayoyi daga wajan yan Jaridu a Minna.

Ya bayyana cewa wadanda ba yan asalin jihar bane an mayar da su zuwa jihohin su na asali.

Dr Muhammad ya kara da cewa kawo yanzu mutane 1,778 aka yiwa gwaji cikin su an samu mutane 166 da suka kamu da cutar.

Gwamnan jihar Abubakar Sani Bello a yayin ganawa da kwamitin karta kwana kan cutar COVID-19 a jihar bisa jagorancin Ibrahim Matane, ya umarci dalibai da ma’aikata su cigaba da kasancewa a gida biyo bayan cigaba da rufe makarantu da ofisoshi, sakamakon karuwar bullar cutar a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: