Garuruwa 3 Sun Rabauta Da Aikin Ruwan Sha A Gwuiwa Ta Jigawa

0 141

Gwamnatin jihar Jigawa ta samarwa da garuruwa uku da ruwansha mai amfani da hasken rana a karamar Gwiwa karkashin aiyukan mazabu.


Haka kuma an tona fanfunan tuka tuka a garuruwan 13
Wakilin mazabar Gwiwa a majalissar dokokin jihar Jigawa Alhaji Aminu Zakar ya sanar da haka.


Yace tuni aka kammala wasu tuka tukan yayinda wasu aiyukan suke daf da kammaluwa.


Alhaji Aminu Zakar ya kara da cewar an gina makarantun islamiyya guda hudu a garuruwan Farad a Kafi naira yawo da Dabi da kuma gimiyar meshaluwa wadanda tuni aka mika su ga alumma.

Dan majalisar wanda kuma shine shugaban kwamitin yada labarai na majalissar dokokin jiha ya yabawa alummar mazabarsa bisa hadin kai da goyan bayan da suke bashi a kowane lokaci.


Yace an gudanar da aiyukan mazabun ne a 2019 yayinda a wannan shekarar ma an tsara yin wasu aiyukan na mazabu amma kuma matsalar cutar corona ta kawo nakasu

Leave a Reply

%d bloggers like this: