Jami’an yan sanda a jihar Kaduna sun kama sama da mutane 217 wadanda aka amince cewa sune da alhakin kashe-kashe, garkuwa da mutane da kuma fashi da makami a jihar.
Cikin wannan makon yan bindiga sun kashe tare da sace mutane da yawa a wasu yankuna da ke jihar.
Kwamishinan yan sandan jihar Umar Muri wanda ya mika wadanda ake zargi ga helikwantar rundunar a kaduna a jiya laraba, ya kuma nuna bindigogi da suka hada AK47 da sauran makamai da aka kwato daga wajan yan bindigar.
- Za’a yiwa mutane 1,000 tiyatar Yanar Idanu kyauta a Jihar Jigawa
- Gwamnatin jihar Jigawa ta tura tawagar kwararru zuwa jihar Edo domin kwaikwayo tsarin koyo da koyarwa
- Sanata Oluremi Tinubu da Nuhu Ribadu za su jagoranci addu’ar neman sauƙi ga Najeriya
- ‘Yan’uwan yaran da aka tsare kan zargin yin zanga-zanga sun nemi ayi musu adalci.
- Koriya ta Arewa ta yi gwajin sabon maƙami mai linzami
Umar Muri ya bayyana cewa an kama wadanda ake zargin tsakanin ranar 29 ga watan afrailu zuwa 22 ga watan yunin wannan shekarar.
Ya kara da cewa haka kuma rundunar ta kwato milyoyin jabin kudade na kasashen ketare da na gida, da kuma buhuhunan shinkafa, motoci, babura, talabijin, wayoyin tarho, kamfuyutoci, shanaye, jabin ID cards na yan sanda, da kuma tabar wiwi daga hannun wadanda ake zargin.