Benjamin Netanyahu zai gana da Donald Trump

0 65

Firaminstan Isra’ila Benjamin Netanyahu zai gana da Shugaban Amurka Donald Trump a Washington a yau domin tattaunawa.

Ana sa ran tattaunawar za ta mayar da hankali kan tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

Mista Trump ya bayyana cewa ya na so yaƙin ya zo karshe, sai dai Netanyahu na fuskantar matsi daga ɓangaren masu tsattsauran ra’ayi kan cigaba da yaƙin har sai an ci galaba kan Hamas.

Gabanin taron, an harbe sojojin Isra’ila biyu kusa da birnin Tabas a gaɓar Yamma.

Lamarin na zuwa ne a yayin da sojojin Isra’ila ke cigaba da kai munanan hare-hare kusa da birnin Jenin.

– REUTERS

Leave a Reply