Kungiyar NULGE ta gargadi CBN kan tauye ‘yancin kananan hukumomi.

0 87

Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomi ta Najeriya (NULGE) ta yi gargadi ga Babban Bankin Najeriya (CBN) da kada ya taimakawa gwamnonin jihohi wajen tauye ‘yancin kananan hukumomi.

Shugaban kungiyar, Hakeem Ambali, ya musanta cewa kananan hukumomi ba su da takardun bayanan kudi na shekaru biyu da suka wuce.

Ya ce dukkan kananan hukumomi suna da akalla bayanan kudaden da suka shafe shekaru uku suna gudanarwa.

Kungiyar ta bukaci CBN da ya bude asusun banki na kananan hukumomi domin su samu kudaden su kai tsaye kamar yadda Kotun Koli ta yanke hukunci.

Leave a Reply