Kotu ta umarci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ta biya diyyar Naira biliyan 1.12

0 80

Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta umarci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ta biya diyyar Naira biliyan 1.12 ga iyalan Mike Madu wanda direban INEC ya kashe a wani hadarin mota.

Alkalin kotun, Mai shari’a Inyang Ekwo, ya bukaci INEC ta biya diyyar tare da karin ribar kashi 10 cikin 100 a shekara har sai an biya duka kudin.

Kotun ta kuma bukaci INEC da shugaban ta su aika da takardar ta’aziyya ga iyalan wanda ya rasu.

Wannan hukunci ya biyo bayan shari’ar da ‘yan uwan Madu suka shigar tun a shekarar 2019 suna neman ai musu adalci.

Leave a Reply