Binciken masana ilimin taurari ya gano wani sinadarin karfe da kimarsa ta zarce arzikin duniya sau dubu 70

0 144

BINCIKEN MASANA ILIMIN TAURARI YA GANO WANI KARFE DA KIMARSA TA ZARCE ARZIKIN DUNIYA SAU DUBU 70

Masu binciken Sararin Samaniya na Kasar Amurka sun gano wani katon karfe dake kewayawa tsakanin duniyoyin Jupiter da Mars wanda suka ce ya kunshi karfe da ma’adanin Nickel wanda ake ganin sai an hada arzikin duniya sau dubu Saba’in (70,000) kafin a iya sayensa.

Masana sunce Wannan katon karfe ya kai girman Birnin Massachusetts na kasar Amurka, inda suka ce fadinsa yakai tafiyar mile 145.

Duba da irin tarin arzikin dake jikin Wannan gungumen karfe an kiyasta cewa zai kai Dalar Amurka quadrillion 10, wanda kimanin ninkin arzikin duniya ne sau dubu 70 kenan, idan akayi laakari da kididdigar shekarar 2019 wanda akace Arzikin duniya baki daya Dalar Amurka trillion 145 ne.

Wannan bincike zai iya yin kamanceceniya da wani bayani da Imam Jafar Alsadiq yayi kancewa ita kanta Wannan duniya da mutane duke Rayuwa a cikinta itace ta karshe a Cikin duniyoyin dubu Saba’in da Allah ya halitta kuma da halittu a cikinsu.

Wannan din dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da Jirgin ‘yan sama Jannatin da Hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka NASA ta harba a ranar litinin mai suna DART ya samu nasarar buge daya daga cikin miliyoyin duwatsun da suke tsala gudu a sararin samaniya.

Nasarar dai ta zama wani gwaji mai cike da tarihi da ke nuna karfin dan Adam na dakile barazanar halittun da ka iya ruguza rayuwa a doron kasa a cewar su.

Tasirin sauyawa dutsen na Asteroid alkibla daga falakin da yake tafiya akai, ya faru ne da misalin karfe 7:14 na yammacin yau a agogon Gabas, watanni 10 bayan da kumbon da NASA ta harba ya tashi daga California don gudanar da gwajinsa na farko.

Lori Glaze, daraktan sashin binciken kimiyar duniyoyin dake sararin samaniya ya ce an shiga wani sabon zamani da dan adam ke da damar kare kansa daga halittu irinsu duwatsun asteroid mai hatsarin gaske.

Jirgin ‘yan sama jannatin yayi taho mu gama da dutsen na Asteroid wanda aka fi sani da Dimorphos mai tsawon mita 160 mai kama da dalar Pyramid na Masar ne cikin tsala gudun kiomita dubu 14 da 500 cikin sa’a daya, karon da ya sauyawa makeken dutsen alkibla.

Bincike dai ya nuna cewar duwatsun asteroids basa zama barazana ga duniyar da muke, domin kuwa falakin da suke tsala gudu akansa na da nisan kilomita miliyan 11 da 265 da 408 da duniyar mu.

Sai dai duk da hakan hukumar NASA ta dauki gwajin karkatar da duwatsun na Asteroids da mahimmanci, saboda gaba.

Irin wadannan duwatsu sun dade suna barazana ga rayuwar bil’adama a doron duniya, domin a cewar hakumar irinsa ne ya taba fadowa wannan duniya shekaru miliyan 66 da suka gabata, wanda hakan ya haddasa wata gobara data shafi ko ina a fadin duniya, har ta haifar da wani hayaki wanda a cewarsu shine ya kawo karewar wata Halitta da ake kira DINOSAURS wato kakan kadangare daga doron kasa.

Koda yake bincikensu yace irin wannan barazana tana iya mai-maituwa bayan kamar shekaru 33 idan ya sake kawo ziyara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: