Fadar shugaban kasar Najeriya ta ce babu wata jiha da aka ba wa izinin siyan makamai masu sarrafa kansu domin tsaronta

0 62

Fadar shugaban kasa ta ce babu wata jiha da aka ba wa izinin siyan makamai masu sarrafa kansu domin tsaronta.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Mallam Garba Shehu, a jiya a wata sanarwa da ya fitar, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha bayyanawa karara cewa babu wanda aka yarda ya dauki bindigar AK-47 ko makamancinta ba bisa ka’ida ba, kuma dole ne ya mika ta ga hukuma.

Gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, a ranar 22 ga watan Satumba, ya soki gwamnatin tarayya bisa adawa da shirin amfani da makamai da kungiyar tsaro ta kudu maso yamma kasar nan, wato Amotekun ke yi, yayin da ta kyale makamanciyar kungiyar tsaro a jihar Katsina ta yi amfani da makamai.

A ranar Litinin ne gwamnan ya bayyana kudirin sa na samar da makamai ga Amotekun domin gudanar da ayyukan tsaro mai inganci wajen tabbatar da tsare rayuka da dukiyoyin al’ummar yankin.

Sai dai a wani martani da ta fitar a jiya, fadar shugaban kasar ta ce a karkashin dokokin da ake da su, baya ga shugaban kasa, ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ne kadai zai iya bayar da irin wannan izini.

Leave a Reply

%d bloggers like this: