Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Damaturu, ta umarci jam’iyyar APC da ta mika sunan Bashir Shariff Machina a matsayin ɗan takarar sanatan Yobe ta Arewa, bayan tabbatar da zaben fidda-gwani da jam’iyyar ta gudanar a ranar 28 ga watan Mayun 2022.

Mai shari’a Fadimatu Murtala, a cikin hukuncin da ta yanke a yau Laraba a Damaturu, ta kuma soke zaben fidda gwani na ranar 9 ga watan Yunin 2022 wanda ya samar da shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan a matsayin ɗan takarar.

Lauyan wanda a ke ƙara na 2, Kolawale Balogun ya shaida wa manema labarai cewa za a ba wa wanda yake karewa shawara kan mataki na gaba.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: