Yadda wata ta kai karar mijinta kotu saboda ya daina cin abincinta saboda zargin zata sanya masa guba a ciki
Mata Ta Kai Karar Mijinta Kotu Saboda Ya Daina Cin Abincinta saboda zargin zata sanya masa guba a abinci, shin ko me yayi mata?
Wata malama mai suna Joy Eze, a ranar Alhamis ta maka mijinta Nuel Chukwu a gaban kotu a Abuja, saboda ya ki cin abincin da take dafawa, saboda yana zargin tana son sanya masa guba.
Misis Eze wacce ke zaune a yankin Jikwoyi a Abuja, ta yi korafi ne a cikin takardar neman raba aure da ta kai wa Chukwu.
A cewarta Ba zata iya ci gaba da zama a karkashin mutumin ba. Da Ya daina cin abincinta kullum cikin zargi, a lokacin data sauke gittere sai yace da ita yana sane da shirinta na son kashe shi.
Har Ya gaya wa danginsa cewa idan ya mutu a kama ta.
Ta kuma shaida wa kotun cewa Chukwu ya juya tunanin yaranta.