Yadda ruwa ya malalo daga Dam din Tiga zuwa garin Haya ta karamar hukumar Gwaram idda ya mamaye tare da lalata dubban kadada na gonakai da dama

0 98

Ruwan da ya Malalo Daga Dam din Tiga zuwa garin Haya ta karamar hukumar Gwaram ta mamaye tare da lalata dubban kadada na gonakai da dama a jihar Jigawa.

Wasu shugabannin al’umma a garin Haya a wata sanarwa da suka fitar sun bukaci hukumar kula da kogin Hadejia/Jama’are da ta sake gina madatsar ruwa ta Haya.

Shugabannin al’ummar sun yi wannan kiran ne a cikin wata takarda, wacca suka rabawa manema labarai mai dauke da sa hannun Malam Muhammadu Lawal Ibrahim kuma aka rabawa manema labarai yau a Dutse.

Ya ce madatsar ruwan da aka gina kimanin shekaru 12 da suka gabata ta ruguje sama da kwanaki uku sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi, lamarin da ya sa ruwan ya yi ta kwarara.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, a lokacin da mazauna yankin suka ga alamun rugujewar Dam din, da dama sun kai rahoto ga hukumomin da abin ya shafa domin daukar mataki.

Ya kara da cewa madatsar ruwa ta inganta zamantakewa da tattalin arzikin mazauna yankin musamman a lokacin noman rani.

Leave a Reply

%d bloggers like this: