Biyo bayan wasu hare-haren yan bindiga a kalla mutane 12 ne suka mutu a jihar Zamfara

0 55

A kalla mutane 12 ne suka mutu a kyauyen Sakajiki na Masarautar Kauran Namoda ta Jihar Zamfara, biyo bayan wasu hare-haren yan Bindiga.

Kakakin rundunar yan sandan Jihar Muhammad Shehu, shine ya tabbatar da hakan ga gidan Talabijin na Channels Tv a jiya.

A cewarsa, adadin mutanen da aka kashe zai fi hakan, inda ba’a tura karin Jami’an tsaro wurin ba akan Lokaci.

Kakakin Rundunar ya ce Kwamishinan Yan Sanda na Jihar Zamfara ya sake tura karin Jami’an tsaro a yankin domin sake karfafa doka.

Wani shaidar gani da Ido, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 9 na Daren ranar Alhamis a lokacin da yan bindigar suka kwashe fiye da a wanni suka harbe-harbe a yankin.

A cewarsa, kimanin mutane 12 ne suka mutu a lokacin, kuma yan bindigar sun cigaba da aika-aikar har zuwa karfe 4 na safiyar ranar Juma’a.

Haka kuma ya ce yan bindigar sun kone shaguna da gidaje, da kuma Ofishin yan Sanda, da kuma sauran ababen hawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: