Jam’iyyar APC reshen jihar Jigawa ta gudanar da zaben shugabanninta na jiha ta hanyar sulhu.

A jerin sunayen wadanda aka zaba, wanda Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafen Sadarwa, Auwalu Danladi Sankara, ya wallafa a shafinsa na Facebook, an zabi Aminu Sani Gumel a matsayin Shugaban jam’iyyar na jiha, yayin da Nasiru Dahiru Jahun ya zama Mataimakin Mataimakin Shugaban jam’iyyar.

Sauran zababbun sun hada da Mannir Uba Gumel, Shugaban jam’iyyar na Arewa maso Yamma, sai Isah Baba Buji, Shugaban jam’iyyar na Jigawa ta Tsakiya, da Abdullahi Ango Malam-Madori, Shugaban jam’iyya na Arewa maso Gabas, da kuma Muhammad Umar Dikuma, a matsayin sakatare.

Sauran sun hada da Umar Musa Kwalgwai, Ma’aji, Bashir A Kundi, Sakataren Yada Labarai, Hajiya Abu S Fawa, Sakatariyar Tsare-Tsare, Ibrahim Ya’u Gagarawa, Shugaban Matasa, Dayyaba Shuaibu, Shugabar Mata, Adamu Haruna, mai binciken kudi, Muttaka Namadi, sakataren walwala, da Badamasi Abdu Chai-Chai, sakataren Kudi, da sauransu.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: