Shahararren limamin coci, Tunde Bakare, ya yi wata ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Bayan ganawar, Tunde Bakare ya shaidawa manema labarai cewa ya tattauna batutuwa daban-daban tare da shugaban kasar, ciki har da bukatar sake fasalin kasarnan da kuma burin siyasarsa a nan gaba.

Tunde Bakare abokin Shugaba Buhari ne kuma abokin takararsa a zaben shugaban kasa na shekarar 2011 wanda ya sha kaye a hannun shugaba mai ci a lokacin, Goodluck Ebele Jonathan.

Babban malamin addinin kiristan, ya yi ta sukar gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ‘yan kwanakinnan.

Lokacin da aka tambaye shi ko zai tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2023, Tunde Bakare ya ki bayar da cikakkiyar amsa, sai dai ya ce ya sanar da niyyarsa ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: