Majalisar Dinkin Duniya ta ce da alama akwai kyakykyawan fatan komai zai dawo daidai a yankin Arewa maso Gabas

0 62

Majalisar Dinkin Duniya ta ce da alama akwai kyakykyawan fatan komai zai dawo daidai cikin shekaru kadan masu zuwa a yankin Arewa maso Gabas.

Da take yi wa manema labarai jawabi jiya a Abuja, Mai Taimakawa Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ahunna Eziakonwa, ta ce an samu gagarumin ci gaba a yankin.

Eziakonwa wacce kuma ita ce Daraktar Yankin Afrika ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce tallafin da Majalisar Dinkin Duniya ke bayarwa ya riga ya kawo gagarumin cigaba.

Eziakonwa wacce tazo Najeriya a ziyarar aiki don samun damar duba sakamakon tallafin Majalisar Dinkin Duniya, duk da haka, tace akwai sauran aiki da yawa da za a yi nan gaba.

Ta bayyana aikin ta a matsayin mai cike da damuwa, kasancewar an haife ta kuma ta girma a Najeriya.

Eziakonwa ta yi nuni da cewa makarantu sun dawo tare da malaman da ke aiki ba tare da matsala ba a kauyukan yankin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: