Ofishin shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cewa nan ba da jimawa ba za a tilasta masa rage rabon abinci ga mata da maza da yara sama da rabin miliyan a Arewa maso Gabas.

Daraktan Shirin na Yammacin Afirka, Chris Nikoi ya fadi hakan cikin wata sanarwa yau a Abuja, bayan wata ziyara da ya kawo Najeriya kwanannan.

Ya ce shirin zai yi haka ne muddin ba a samu tallafin gaggawa ba, domin cigaba da ayyukan ceton rayuka a jihohin Borno, Yobe da Adamawa.

Daraktan ya bayyana cewa ragin zai zo daidai lokacin da ake fama matsananciyar yunwa mafi muni cikin shekaru biyar a kasarnan, sakamakon rikice-rikice da rashin tsaro.

Ya ce lamarin ya kara ta’azzara sakamakon tabarbarewar zamantakewa da tattalin arziki sanadiyyar annobar corona da hauhawar farashin kayan abinci da kuma karancin abincin.

Ya kara da cewa adadin mutanen da suka rasa muhallansu ya haura miliyan biyu zuwa watan Satumbar da ya gabata.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: