Gwamna Elrufa’i ya bayyana dalilin kirkirar Hukumomin Lura da Cigaban Biranen Kaduna, da Zaria da kuma Kafanchan

0 97

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i ya bayyana dalilin kirkirar Hukumomin Lura da Cigaban Biranen Kaduna, da Zaria da kuma Kafanchan.

Mutane da dama ne suka bayyana adawar su kan kirkirar hukumomin cigaban biranen 3 tare da nada masu kula da su.

Wasu na ganin cewa hakan kamar karbe ikon Kananan Hukumomi ne daga hannun su.

Sai dai da yake rantsar da Sabbin Alkalai biyu a jiya, Gwamna El-Rufa’i ya bayyana cewa sabbin hukumomin da aka kirkira masu kulawa da cigaban biranen uku, babu ruwan su da Majalisun Kananan Hukumomi.

A cewarsa, ayyukan su shine kulawa da cigaban manyan Biranen da suke Jihar tare da ciyar dasu gaba.

Gwamna El-Rufa’i ya ce nauye-nauyen da aka Dorawa Hukumomi basa kamanceceniya da na Kananan Hukumomi.

Kazalika, ya ce ayyukan hukumomin cigaban biranen Zaria, da Kaduna da kuma Kafanchan, su zasu zama tamkar ayyukan Ministan Birnin tarayya Abuja.

Leave a Reply

%d bloggers like this: