Jagoran Jam’iyyar APC na Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce Allah na iya bayar da mulki ga duk wanda yaga dama.

Bola Tinubu ya fadi haka ne jiya a Legas yayin da ya sake haduwa da abokan siyasarsa da masu kare shi a wani taron maraba da addu’o’i, wanda Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya shirya.

Taron shine farkon fitowar Tinubu tun bayan dawowarsa daga Burtaniya a daren Juma’a, bayan watanni uku ba ya kasar.

Jagoran Jam’iyyar APC na kasa, wanda rahotanni ke cewa yana sha’awar neman kujerar shugaban kasa a shekarar 2023, ya ce abin da Allah ke bukata daga duk wanda Ya ba shi mulki shi ne ya amfanar da mutane.

Ya ce taron addu’ar ya kasance mai soyuwa a gare shi, yayin da fatan alheri daga ‘yan Najeriya da suka yi masa fatan alkhairi yayin da ba ya nan.

Gwamna Sanwo-Olu ya ce dawowar Tinubu labarine mai faranta rai ga magoya bayansa a duk fadin kasarnan.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: