Kungiyar Tarayyar Afirka ta ce tana son karawa da fadada aikin sojinta a kasar Somaliya, inda dakarunta suka shafe shekaru 14 suna yaki da masu kaifin kishin Islama.

Kungiyar ta ce za a gudanar da sabon aikin ne tare da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya.

Ta ce fadada rundunar ta Amisom za ta hada da sojoji daga wasu kasashen Afirka.

Akwai bukatar amincewar Majalisar Dinkin Duniya da gwamnatin Somaliya, wadanda a baya suka yi watsi da shawarwarin Kungiyar Tarayyar Afirka.

Kasar Habasha, wacce ke ba da gudummawar dubban sojoji ga Amisom, na fuskantar manyan kalubalen tsaro a gida.

An kuma bayar da rahoton cewa kasar Kenya na duba yiwuwar rage sojojinta.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: