Jami’an Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) a yau sun kai farmaki a helkwatar hukumar raya birane ta jihar Kaduna inda suka yi awon gaba da Darakta Janar na hukumar, Malam Ismail Umaru Dikko.

Hukumar ta yi kaurin suna a matsayin wacce aka fi jin tsoro a Kaduna saboda rushe gine-ginen da ta yi a fadin jihar.

Darakta janar na hukumar, Ismail Dikko, ya kasance mataimaki na musamman ga gwamna Nasir El-Rufai, kafin a kara masa matsayin zuwa shugaban hukumar a shekarar 2019.

An rawaito cewa Darakta Janar na cikin ganawa da ma’aikatan sa lokacin da jami’an EFCC suka mamaye harabar ofishin ‘yan mintoci kadan bayan karfe 10 na safe.

Shaidun gani da ido sun ce an yi wani hargitsi kafin Darakta Janar ya shiga wata bakar mota kirar Toyota ta EFCC.

Majiyoyi sun ce jami’an EFCC guda biyu tare da ‘yan sanda biyu dauke da bindigogi sun raka Darakta Janar cikin motar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: