Gwamnatin tarayya ta shirya kashe naira miliyan 650 a matsayin kasonta na aikin samar da wutar lantarki na Mambilla

0 94

Gwamnatin tarayya ta shirya kashe naira miliyan 650 a matsayin kasonta na aikin samar da wutar lantarki na Mambilla a cikin kasafin kudin shekarar 2022.

Aikin, wanda aka dade ana kokarin aiwatarwa, yana cikin ayyukan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sanya a gaba.

Sai dai, cikin kiyasin kasafin kudin, gwamnati ta ware naira biliyan 1 da miliyan 600 don ci gaba da sauye-sauyen motoci da kayayyakin gyaran motoci a fadar shugaban kasa.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da ma’aikatar wutar lantarki ke da kasafin kudi na naira biliyan 301 na shekara mai zuwa, wanda ya haura naira biliyan 204 a shekarar 2021.

Daga cikin ayyukan da ke jan kafa, aikin na Mambilla zai lakume naira miliyan 650. Hakan duk da kasancewar an kashe kudi sama da naira biliyan 10 akan wannan aikin a cikin shekaru shida da suka gabata ba tare da an fara aikin ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: