Shin da gaske ne za a rufe manhajar WhatsApp?

0 84

Ba gaskiya ba ne cewa wai za a rufe Whatsapp kamar yadda ake ta yada wani sauti (audio) a kafafen sadarwa.Irin labarin nan ne na karya, irin wanda ake kirkira a duk lokaci da wani ya faru don a rudar da mutane (misinformation), tun daga lokacin da aka samu tangarda tsayawar manhajojin Facebook, Whatsapp da Instagram na ‘yan awanni a cikin satin da ya wuce.

Babu wani rahoto ko sanarwa daga kamfanin Mark Zuckerberg, ko wata hukuma ko kafa mai kula da al’amuran sadarwa dake tabbatar da hakan.Abin da yake sahihi shi ne, akwai wasu samfurin wasu wayoyi da Whatsapp zai daina aiki a kansu a cikin watan November mai zuwa, daga ciki har da iPhone SE, iPhone 6s, iPhone 6, Samsung Galaxy S3 da sauran tsofaffin wayoyin Samsung, LG, ZTE, Huawei da aka gina tsarinsu akan Android 4.0.3 Ice Cream Sandwich, iOS 9, da KaiOS 2.5.0.Ku tambayi kanku, wai shin mai wannan maganar waye? Amsa, baka san waye ba. Wani ya rubuta Turanci, ya saka a ‘Google Text-to-Speech’ (manhajar da ke karanta rubutu cikin sauti), sai ya yi recording yake yadawa mutane. Kar kai ma ka taimaka wajen yada labari maras sahihanci don rudar da mutane. Mu taimaka wajen yaki da labaran karya, musamman a media.

(c) Aliyu M. Ahmad

Leave a Reply

%d bloggers like this: