Kakakin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan Kafafen Yada Labarai Mista Femi Adesina, ya kare gwamnatinsa, inda ya ce gwamnati Shugaba Buhari bata gaza ba.

Da yake jawabi ga gidan talabijin na Channel Tvta cikin shirin Politics Today, Mista Adesina, ya ce wanda suke ganin gwamnatin Shugaba Buhari ta gaza sunyi kuskure.

Mista Adesina, ya ce shugaba Buhari ya cika wasu daga cikin Alkawarirrikan da ya dauka a lokacin yakin neman zabe wanda suka hada da yaki da rashawa da inganta tsaro da kuma bunkasa tattalin arziki.

Haka kuma ya dage cewa gwamnatin tarayya ta samu nasarori a fannin tsaro fiye da gwamnatin da suka gada a baya.

Kakakin Shugaban Kasar ya ce a lokacin da suka shiga gwamnati matsalolin hare-haren yan kungiyar Boko Haram ne ya fi addabar mutane fiye da yan bindiga da masu Garkuwa da mutane.

Kazalika, ya ce gwamnatin tarayya ta damu da yanayin da tsaron kasar nan yake ciki, kuma tana iya bakin kokarinta wajen magance matsalolin tsaro.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: