Jam’iyar APC ta kaddamar da Kwamatin Sasanto mai mutane 9 domin hakurkurtar da yayan Jam’iya.

A cewar Jam’iyar, hakan yana daga cikin kokarin da take yi domin ganin ta sake gyatta zaman Jam’iyar kafin gudanar da gangamin ta na Kasa da kuma zaben shekarar 2023.

Da yake Jawabi bayan kaddamar da Kwamatin Shugaban Jam’iyar na Kasa Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe, ya bukaci kwamatin ta sasanta ya yan Jam’iyar.

Haka kuma ya bukaci Kwamatin ya yi kokarin fito da hanyoyin sasanta mambobin Jam’iyar domin kawar da bam-bamce bam-bamcen dake tsakanin su.

Kwamatin yana karkashin kulawar tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa Sanata Abdullahi Adamu, inda kuma Mista Moses Adeyemo, ke zaman sakataren Kwamatin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: